Monday, April 16, 2007

Wasiyya Sipikiyya; Daga Mudi Spikin

Ta'ala ina rokonka ranar da zan cika
Kasa in cika Allah cikin daki na

Gaban duk iyali na da 'ya'ya da 'yan'uwa
Allah ina rokon ka sai a gidana

Idan na cika yan'uwa na gaya muku
Da kun ji cikawata ku taru gidana

Idan har da rana abin yazo ko cikin dare
Batun jinkiri kar dai ya faru wurina

Idan anyi sallah an gama kar a dakata
A dauka kawai hanyar zuwa kabarina

Idan anka je da zuwa a sani ciki kawai
Cikin hankali domin tuno lamarina

Kasar kabarin kuma kar a ware daban-daban
A turo gaba daya duk ta watsu a kaina

Idan aka kare gini da an tashi an gama
Ku koma wajen harkarku ya jama'ata

Batun sadakar Uku, ko Bakwai, ko ta Arba'in
Kaza shekara wallahi babu ruwana

Irin masu kukan nan da ihu da razana
Don Allah na roke ku kar kuyi kaina

Ina tausayin ku kwarai zuwa gun jana'iza
Kaza wahalar tafiya hakan kabarina

Kaza wahalar wanka da dauko ni don zuwa
Cikin makara tafiya zuwa karshe na

Hakika a rannan da da ikon da zan iya
Ya sa tausayin a wajen dukan jama'ana

Anan zan tsaya domin wasiyarmu ta tsaya
Mudi Spikin ne uba ga Amina

Wakar Shehu malam Nasara Kabara; Daga Mudi Spikin

Bagadada suna ajabi nasa
Don sun ga irin himma tasa
Suka ce kai wannan ya isa
Har yanzu suna Allah yasa
Su ga Alhaji malam Nasiru

Qadiriyya yai zurfi ciki
Darajarta kwarai yai arziki
Jama'a da yawa duk sun saki
Hairi a gare shi daki-daki
Kuma ga takawa gun Nasiru

Shi gwarz ne mai kokari
Mai kamala mai kyawon shiri
Ga mutunci gashi da hankuri
Ko ina an san shi gari-gari
Kwarjini sai Malam Nasiru

RASHA Abokan Fita Kunya; Daga Mudi Spikin

Wannan waka ta jawowa Malam Mudi dauri a gidan yari. Domin a fahimtar Turawan Mulki wannan wani sako ne da kan iya tunzura talakawa suyi bore, kuma kan iya jefa kasa cikin juyin-juya hali irin na Kwaminisanci. Mudi Spikin ya rubuta wannan waka a 1948. Ga dai wakar

Ya yan'uwa ku zo don ku ji ni
Zan wo bayani akan Rusiya

Gama Ingilishi fa sun tashi haikan
Suka suke yi akan Rusiya

Da babbata hanyarsu don kar a so su
Don kar su zo nan mutan Rusiya

Shine nake so in wo dan bayani
Domin ku gane kasar Rusiya

Kasa ce ta kirki da himma garesu
Da kaunar mutane kasar Rusiya

Wakilinsu Malik sunansa ke nan
Sunan musulmi da ba fariya

Ni dai ace yau zan samu iko
Ni sai in koma kasar Rusiya

Kamar na iya tsunts inje can in Zauna
Idan na tuno su mutan Rusiya

Girmama kowa dabi'arsu ce
Ibada kamar Hajji sai Rusiya

Da son musulunci da bayar da zakka
Yawan azumi sai kasar Rusiya

Kwalta na banza damu bamu samu
Da kafur akeyi acan Rusiya

Da banki na rance idan har kana so
Ko fam Dubu Goma baki daya

Musaki acan sai ya zauna da Gwamna
Wajen shawara babu kin gaskiya

Sa'annan da sauran abubba na kirki
Suna da yawa a kasar Rusiya

Gidaje dubu Goma ne don Musakai
A yau su kasar wane ba ko daya

Akwai Talakawa akwai Tajirai
Kamar dai kasarmu ta Nijeriya

Anan gaba na tabbata babu shakka
Nijeriya zamu zam Rusiya

Mu zam mun fice daga gun Ingilishi
Mutanen daba sa rikon gaskiya

Sun barmu babu kudi babu gona
Babu abin yi cikin gaskiya

Sun shekaru yanzu Hamsin kasarmu
Ba taimako babu son gaskiya

Ta'ala Rahimu kadai taimakemu
Ka kawo mutan Rasha Nijeriya

Idan aka ce wa ya tsara ta waka
Ya bayyana halin mutan Rusiya

Ba zan boye suna ba ko za'a nema
Mudi spikin maso Rusiya

Gama bani tsoro na dauri hakika
Akan Rasha ma sai in bar duniya

Karara; daga Malam Mudi Spikin

An haifi Alhaji Mudi Spikin a ran 1 ga watan Oktoba 1930, a unguwar Darma da ke birnin Kano. Yayi karatun qur'ani a hannun Malam Umaru Badamagare. Bai taba zuwa makarantar boko ba, amma duk da haka, ya zauna jarrabawa GCE Ordinary level, ta hanyar yin rijista da wata kwaleji a Ingila, acikin 1960. Ya sami illimin zamani ne a hannun abokansa na gwagwarmayar siyasa irinsu; Malam Sa'adu Zungur, Malam Aminu Kano, da kuma Alhaji Yusuf Maitama Sule. Yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar kwato yancin talaka wato NEPU a 1950. Ya fara rubuta wakokinsa tun a 1948, ya fara da wakarsa ta "Rasha Abokan Tafiya", da kuma wani raddi da yayiwa malaminsa, wato malam Sa'adu Zungur maitaken "Arewa Jamhuriya Kawai".

A ya jama'a ina tashin
Ku dan ku rage yawan bacci

Ayau na zo gareku da sha
Wara don kara inganci

Mu wo himma mu tashi tsaye
Mu gyara kasa ta san yanci

Mu kawo shawara mai kyau
Mu tashi mu yaki jahilci

Rashin illimi ya sanya yau
Kasar nan ke yawan baci

Fa sai mun tsaya gyara
Na sosai babu jahilci

Sannan zamu san matsayi
Mu tsere wa wulakanci

Idan ba tattali a kasa
Hakika dole ta baci

Idan an zubda hakkin yan
Adam domin wulakanci

Idan masana kwarai an zub
Da su domin rashin yanci

Idan sharia ta zam ciniki
Ana nunnuna bambanci

Idan kuma masu aiki sun
Zamo duk babu inganci

Idan aiki ya zamto ba
Ayi, sai an ciwo hanci

Idan hairi a baki ake
Fada sharri cikin zuci

Idan da akwai yawan hassada
Da bata mutum da iskanci

Idan da akwai yawanta saki
Na aure don wulakanci

Idan ba tanadi wai duk
Wata sai anyi angwanci

Idan aure ya zam a kasa
Ana yi ne da jahilci

Idan kayan biki aka mai
Da su tamkar na dillanci

Idan ga jahilai a kasa
Na kin canji da shashanci

Idan da zama na banza, ba
Sana'a ai ta kakaci

A sa fatala gaban goshi
Da hula wai tsageranci

Ana ta musu ana karta
Ana zance na wawanci

Idan kuma ga yawan zargi
Na banza ga rashin yanci

Idan wani dan'uwa wai yayi
Samu ayi munafunci

Idan sharri ya zo a iza
Nufi dai ayi wulakanci

Idan da akwai yawan camfi
Da bori masu shashanci

Idan da akwai yawan tsegun
Guman banza na jahilci

Idan a kasa ya zam an go
Yi bayan masu lalaci

Idan mai gaskiya ya zamo
A kullum zai ga kaskanci

Idan gata ya sanya wadan
Su yin shirme da shashanci

Idan aka maida wadansu kamar
Ace bayi rashin yanci

Idan yan kasuwa suka zam
Sana'a aita hainici

Idan ga karuwai a kasa
A kullum ai ta fasicci

Idan da giya an ta
Ru kullm nuna iskanci

Idan ba tausayi a kasa
Mutane na ta makirci

Idan kuma har amana tai
Kadan sai nuna ha'inci

Idan har maluma suka bar
Sani i zuwa fagen baci

Idan bidia ta zam an gir
Gina kuma babu sassauci

Idan yaya suna sabon
Mahaifa har da kaskanci

Idan a kasa akwai wannan
Hakika dole ta baci

Fa sai in anyi aiki za
Hiri ba nuna lalaci

Sa'annan zamu san haske
Mu tserewa wulakanci

Abinda na farfadan nanYan
'Uwa da akwai muhimmanci

Fa duk gyaran wadannan na
Garemu cikin batun yanci

Mu daina abinda bashi da kyau
Mu daina biyewa jahilci.